Spread the love

Wani rahoto mai tayar da hankali daga Ibadan, Jihar Oyo: Rundunar ‘Yan Sanda ta jihar ta ce, ta ceto matasa 19 ƴan Ghana da aka jefa cikin hadarin safarar mutane, bayan an ruɗe su da alkawarin samun aiki mai kyau a Najeriya.

A cikin sanarwar da kakakin rundunar, Adewale Osifeso, ya fitar a ranar Lahadi, ya ce waɗannan matasa, 14 maza da 5 mata, sun faɗa tarkon wasu gurbatattun mutane da suka mayar da su hanyar samun kuɗi ta haram

“An samu bayanan sirri kan wasu ayyuka masu ɗaukar hankali a wani gini a unguwar Kajorepo, Akinyele, Ibadan. Mun kutsa ciki tare da ƙungiyoyin tsaro na musamman, kuma hakan ya taimaka wajen kubutar da waɗannan matasa,” in ji Osifeso.

Bayan an ceto su, an mika su ga Hukumar Shige da Fice ta Najeriya (NIS) domin gudanar da ƙarin bincike da kuma yiwuwar mayar da su gida Ghana su haɗu da iyalansu.

Rundunar ƴan Sanda ta Jihar Oyo ta sha alwashin ci gaba da bincike domin gano duk masu hannu a wannan aika-aika, tare da tabbatar da cewa an gurfanar da su a gaban kotu domin fuskantar hukunci.

About Author

Admin

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *