KMT ya bawa kowace ɗaya daga cikin gwarazan gasar turanci ta duniya Naira dubu 500 da kwamfuta
Alhaji Barista Kashim Musa Tumsa MFR, ya bawa zakarun gasar turanci ta duniya (TeenEagle) kyautar Naira dubu ɗari biyar (500,000) a kowace ɗaya daga cikinsu haɗe da kwamfuta sabuwa dal.
KMT ya ba da kyautar ne a ranar Litinin (29/09/2025) a taro na musamman da aka shirya musu, don miƙa musu kyautar a harabar makarantar ta NTIC da ke Mamuɗo, ƙaramar hukumar Potiskum a jihar Yobe.
Hajiya Kaka Ahmad Abubakar, ita ce ta wakilci Alhaji Kashim Musa Tumsa a wajen taron. A lokacin da take gabatar da jawabi, Kaka ta bayyana wasu daga cikin irin ayyukan alheri da KMT ɗin yake yiwa al’umma a ɓangarori daban-daban a faɗin jihar Yobe.
Ta bayyana yadda ya ɗauki nauyin rubuta jarabawar JAMB a ɗalibai da dama a jihar. KMT ya bawa ɗalibai 29, Naira dubu ɗari-ɗari a kowannensu, waɗanda suka samu maki sama da 300 a jarabawar JAMB. Ya tallafa wa ɗaliban SUG (Student Union Government) da kuɗi Naira 200.
Hajiya Kaka Ahmad ta bayyana irin gagarumar gudummawa da KMT yake bawa harkar ilimi a jihar Yobe.
KARANTA: Mu na goyon bayan shirin Tinubu na ciyo bashi – Shugaban Majalisar Wakilai
KMT ya bawa shugaban makarantar ɗaliban NTIC (Principal) Naira 250,000. Sannan ya bawa Malaman ɗaliban su uku Naira 150,000 a kowannensu.
Shugaban makarantar (Principal) Habibullah Jogi, ya yi godiya ga Kashim Musa Tumsa, inda ya bayyana shi da mai son ci gaban ilimi, ya yi masa fatan alheri.
Nafisa Aminu, ita ce ta yi godiya a madadin gwarazan gasar, ta nuna farin ciki matuƙa, sannan ta yi godiya ga KMT na irin wannan gudumawa da ya ba su. “Irin wannan shi ne zai ƙara mana ƙarfin gwiwa da dagewa a karatu”